February 01, 2021

Hanyoyi 6 Da Za Ka Bi Don Samun Adsense Approval Cikin Sauki

Shin bukatarka samun adsense approval? In kuwa har haka ne cikin farin ciki nake maka barka da zuwa shafi na.

Samun Adsense Approval

Ka fara karatun wannan rubutu ne a shafin Abba Abdullahi Garba, in ka samu dama ka yi sharhi a wannan rubutu nawa.

Da dama daga cikin abokai musamman masu ikirarin sune arewa bloggers suna yawan kawomin korafin kasa samun adsense approval a blogs nasu.

Bisa wannan dalili, yasa naga ya dace na wallafa salo da kuma dabarun da nake amfani da su wajen samun adsense approval hankali kwance.

Amma fa ku sani, komai sai da yardar Allah ya ke tabbata, ba salo da dabaru kadai kake bukata ba kafin ka samu adsense approval.

Ya kamata ka dan rinka gaurayawa da addu'a, kunsan ita maganin masifa ce, kuma katangar karfe ga daukacin musulmi.

Duba da yadda adsense suka canza policy dinsu na 2020 wadda ya fara aiki a 2021, samun approval a shafin hausa zai yi wuya.

Amma fa ni ina tunanin hakan bai zams wata matsala ga hausa bloggers ba, domin a shekarar 2020 karshe-karshenta na samu approval.

Haka kuma a 2021 na samu approval na adsense, kuma duk shafuka na ne.

Zan so na kara wa mai karatu haske akan adsense amma kafin nazo nan wurin, bari na baka wani dan karamin labari.

**** Dan Karamin Labari ****

_Na sayi domain a watan december 2020, na saka masa suna THN, kuma "TOP HAUSA NOVELS" shine title dinsa_

_Na fara dora novels a shafin amma a document suke, to kafin na yi hakan sai da na fara neman table code wanda zan rinka jera details din kowanne littafi a ciki_

_Design din shafin, tsarashi, yin posting a cikinsa, da gina masa source of traffic ya daukeni kusan 2 month_

_ Kwana shafin 30 na yi apply na adsense da domain din, sai suka dawo min da shi, alamun ba za su karbeshi ba_

_Alhali hotuna da komai na kammala tsarashi yadda ya kamata, bana amfani da copyright graphics, balle kuma saka bad links a posts nawa_

_Da na kara masa contents, na sabunta design dinsa, ya samu isasshen traffic, bayan na kara apply suka approve dinsa, har shafin ya fara kawo mula_

_Cikin kwanaki 53 na kammal duk wadannan abubuwan, kuma na ji dadin hakan kwarai da gaske_.

***

Akwai wani abu da ya kamata ku fahimta a labarin nan, na bude shafin novels, kuma description dinsa da hausa nake, amma karashen details din na turanci ne.

In har kana son approval, kawai ka kera shafinka ya tsaru, ka tabbatar yana samun enough organic traffic, kuma ka tabbatar unique content ne da kai.

Domin warware ma mai karatu wani abu zan so ya san cewa; Adsense suna karbar shafukan hausa, amma ba wanda aka yi hausa gaba daya a cikinsa ba.

Hakan na nufin "if you can hada hausa da turanci, nobody will kureka da gaggawa". 

Ta wannan salon ne kadai za ka iya samun approval a shafinka a shekarar 2021.

Domin takaita tsayin rubutun bari na fada maka wasu abu guda shida da za ka kiyaye domin samun adsense approval cikin sauki.

  1. Ka yi amfani da template mai kyau a shafinka 
  2. Ka saka about, contact, privacy policy da dmca pages a shafinka 
  3. Ka yi post mai kyau, banda satar post din wasu shafukan 
  4. Ka yi amfani da original photos, banda copyright graphics 
  5. Ka tabbatar shafinka yana samun ingantaccen traffic 
  6. Kada ka yi post din batsa, makamai da sauran illegal contents a shafinka.

Ko wanne abu da na fada a wannan jeri zan maka bayani dalla-dalla akansa, fatan zai amfaneka.

1. Ka yi amfani da template mai kyau a shafinka

Samun adsense approval bai danganta da blogging platform din da kake ba, walau blogger ko wordpress, kawai kana bukatar template mai kyau.

Ba na tunanin za ka samu adsense approval da wani jigari-jigarin template a blog dinka, kana bukatar responsive da good looking template.

Wasu suna amfani da free templates, amma fa a shawarce ku nemi premium templates ku dora a shafinku.

Kuma ku tsara shi yadda ya kamata, hakan zai bada gudunmawa sosai wajen samun adsense approval a shafukanku.

Sannan, ya kasance template din baya da nauyi, ma'ana yana da speed mai inganci, kuma yana da navigation mai kyau.

Insha Allah, indai ka saka template mai kyau mara haske da yawa adsense za su yi approve na shafinka.

2. Ka saka about, contact, privacy, disclaimer da dmca pages a shafinka

Yana daga cikin kuskuren da wasu ke dirkawa kenan, ba sa saka about pages a shafukansu suke apply na adsense.

Ba na tunanin za su yi approve na shafinka muddin ba ya da about us, contact us, privacy policy, disclaimer pages in da hali ka hada har da dmca pages.

In dai ka saka musu wadannan pages din, kuma ka saka links dinsu a navigation menu din shafinka, hakan zai kara adadin damar samun adsense approval din shafinka.

3. Ka yi post mai kyau banda satar post din wasu

Ina mamaki ganin yadda wasu ke yin copy paste na post din wasu shafukan zuwa shafukansu.

Ka manta menene blogging ne? Rubutu za ka rinka yi mai amfani, ba wai ka zuba ido kana kallon wani yana wallafa post mai kyau kai kuma kana binsa kana sace masa ba.

In har so kake ka samu karbuwa a wurin google adsense, yana da kyau ka rinka rubuta posts dinka da kanka.

Domin mutane za su so ziyartar shafinka in dai yana da original contents masu daukar hankali da amfani.

Akwai hanya da za ka bi wajen gane ko post din shafinka na wani ne ka sata ko kuma ya satar maka, ta hanyar amfani da shafin copyscape.

Mai karatu indai adsense approval kake so, kawai ka rubuta posts masu amfani, kuma original a shafinka tukunna.

4. Ka yi amfani da original photos, banda amfani da copyright graphics

Kunsan masu iya magana sunce; Marar shi baya zuciya, hakan na nufin domin ka samu shiga a wurin adsense dole za ka bi dokokinsu da fari.

Eh mana, ka na amfani da apps na graphic design irinsu pixellab, picsart, canva da sauransu kana hada graphics din da za ka rinka saka wa a shafinka.

In dai original graphics kake amfani da su, ina da yakinin za ka samu approval cikin sauki da yardar mai sama.

Amma ko da kana da original posts yma graphics din ba original bane, bana da tabbacin za su yi approval din shafinka.

Duk da haka, kunsa abin rabo ne.

5. Ka tabbatar shafinka yana samun ingantaccen traffic

Wato 'dan uwa babu wani 'dan adam da zai rayu ba tare da abinci ba, don haka babu wani blog da zai ginu ba tare da traffic ba.

Hakan na nufin muddin shafinka baya da makaranta to babu wanda zai ga ads dinka balle ya bude su.

Kuma hakan ya kara nuna cewa shafin bai gama cika sharuddan samun approval ba.

In har kana son adsense approval, kamata yayi ka fara gina shafin, sannan ka nemi adsense.

Kuma organic traffic yafi bada gudunmawa wajen samun approval, amma fa ko babu shi referral ma yana taimakawa sosai.

Bisa wannan dalili, na ke baka shawara lallai ka gina shafin ka yadda ya kamata kafin ka nemi adsense su fara dora masa tallace-tallace.

6. Kada ka yi post din batsa, makamai da sauran illegal contents a shafinka

Nan ma kuma anzo inda yafi kai-kai ga arewa bloggers, domin na san da dama daga cikinsu banda sharri da kage ba abinda suka iya.

In kaga wani title din kai ka rantse mala'iki mai daukar rai ba zai ziyarci mutum ba wata rana.

A shawarce: indai so kake ka samu approval na adsense kada ka rinka post din batsa a shafinka, ko na makamai, ko na kayan sata irinsu (cracking, modding) da sauransu.

Ina da yakinin hakan zai taimaka sosai wajen saukaka maka samun adsense approval.

******

Ba a iya nan na so tsayawa ba, amma babu yadda na iya a nan zan karkare wannan rubutu nawa.

Ga masu tambayata, kuma su yi comment a wannan rubutu zan yi iya kokari na wajen ganin na basu sahihiyar amsa.

Duk mai neman approval ina masa fatan nasara, Allah yasa a dace ameen.

Post a Comment