January 31, 2021

Abinda Ya Kamata Ka Sani Game Da TOP HAUSA NOVELS da Mawallafinsa

Za ta iya yiwuwa kana son sanin wadanda suke da mallakin shafin Top Hausa Novels kuma suke tafiyar da shi.

Kafin na ce komai, ina maka lale marhaba da zuwa wannan karamin blog nawa. 

Sunana Abba Abdullahi Garba, a cikin wannan dan takaitaccen rubutun zan maka cikakken bayani akan dalilin da yasa na bude shafin Top Hausa Novels.

In har neman mai shafin kake to kazo gida, THN mallakin Abba Abdullahi Garba ne, kuma an bude shafin a karshen shekarar 2020.

Da farko lamarin akwai wahala, na shafe watanni biyu ina aiki ba-dare-ba-rana domin ganin shafin ya cimma gaci.

Shafin cikin yardar Allah ya kafu kuma ya tsaya da kafarsa, kuma har yanzu ina kan gina masa backlinks, domain authority da sauran dabarun SEO.

Tun wajen 2016 nake da sha'awar karatun littafan hausa, kuma nake son bada tawa gudunmawar wajen ganin na saukakawa masu karatun novels.

Ina da sanin cewa, mafiya yawancin masu karatu da littafan hausa musamman na soyayya mata ne.

Kuma masu son karatun littafan yaki maza ne mafiya yawancinsu

Amma wannan ba shine matsala ta ba, domin ko littafin waye, indai ka bida za mu siyeshi mu dorashi a shafinmu domin farin cikin maziyartansa.

Har-ila-yau in har kai marubuci ne, kana son dora littafinka a shafin THN, kofa a bude take.

Bisalam, mu huta lafiya.

Post a Comment